10 Nuwamba 2019 - 05:23
Iran Ta Kai Ga Tatse Urenium Da Kashi 5%

Jamhuriya musulinci ta Iran, ta sanar a yau Asabar cewa ta kai ga mizanin tatse sinadarin uranium da kashi biyar cikin dari.

(ABNA24.com) Jamhuriya musulinci ta Iran, ta sanar a yau Asabar cewa ta kai ga mizanin tatse sinadarin uranium da kashi biyar cikin dari.

Da ya ke sanar da hakan, yayin wani taron manema labarai, kakakin hukumar makamashin nukiliya na kasar ta Iran, Behrouz Kamalvandi, ya ce a yanzu Iran, ta kai ga tatse sinadarin uranium a mizanin kashi 5%, kuma a cewarsa Iran din na da karfin da zata iya wuce hakan zuwa kashi 20% , 60% kai fiye da hakan ma.

A ranar Alhamis data gataba ne mahukuntan na Teheran suka sanar da cewa aikin tashe uranium a tashar Fordo, ya kankama, ta yadda na’urorin tatse sinadarin na uranium zasu iya tatse uranium zuwa mizanin kashi 4,5% daga ranar Asabar.

Wannan na daga cikin matakan da Iran din ta ke ci gaba da dauka na kauracewa aiki da wasu daga cikin alkawullan data dauka a cikin yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma da ita a shekara 2015, a matsayin maida kan matakin Amurka na ficewa daga cikin yarjejeniyar.

Tuni dai sauren kasashen da suka rage a yarjejeniyar da suka hada da Faransa, jamus da Biritaniya, suka bukaci Iran data dawo kan matakin data dauka na tatse sinadarinna uranium a tashar ta Fordo.






/129